Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amira Rabi'atu Ta Ce Hakki Ne Kan Musulmi Ya Zauna Da Kowa Lafiya


Musulmi su na sallar Idi a babban Masallacin Abuja, Najeriya, 30 Agusta 2011
Musulmi su na sallar Idi a babban Masallacin Abuja, Najeriya, 30 Agusta 2011

Shugabar Kungiyar Musulmi ta Taimakon Mata da Marayu da Matasa ta ce zuciya mai lafiya, tana sa a zauna lafiya da duk wata halittar da Allah Ya yi

Shugabar Kungiyar Musulmi ta Taimakon Mata da Marayu da kuma Matasa a Najeriya, Amira Rabi'atu Sufyan Ahmad, ta yi kira ga Musulmin Najeriya, musamman na Arewa, da su yi amfani da wannan wata na gafara da rahama, wajen tsarkake zuciya da karfafa zaman so da mutunta juna da sauran jama'a.

Amirar ta ce Allah Ya halicci mutane dabam-dabam, Ya ba su harsuna dabam-dabam, da zabin bin addinai dabam-dabam, da launi da kuma siffa dabam-dabam, domin su zauna da juna su fahimci junansu.

Ta ce Allah ne Ya halicci kowa da komai, yake da iko a kan kowa da komai, don haka ya zamo wajibi mutum ya sao sauran halittun da Allah Yayi.

Ta ce Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) yace imanin mutum ba zai cika ba, har sai ya so ma dan'uwansu abubuwan alkhairi da yake so ma kansa. To wajibi ashe dukkan al'umma na duniya su zauna zaman lafiya da junansu, a samu zaman lafiya a kowane gida da unguwa da gari da kasa a duniya.

Ga cikakken bayanin Amira Rabi'atu Sufyan Ahmad.

Amira Rabi'atu Sufyan Ahmed Ta Ce Allah Ya Halicci Jinsuna Don Su San Juna Ne - 3:21
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG