Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Sama Da Mutane 200 a Zimbabwe


Wata ambaliyar ruwa da ta mamaye wani Lardin Giang
Wata ambaliyar ruwa da ta mamaye wani Lardin Giang

Ambaliyar ruwa a kudanci da kudu maso gabashin kasar Zimbabwe ya kashe akalla mutane 246 tare da lalata gidaje sama da 2000.

Gwamnatin kasar ta Zimbabwe ta tsunduma cikin matsalar karancin kudade, lamarin da ya sa ta nemi taimakon kasashen duniya dalilin wannan ambaliya.

Jami’ai sun ce ambaliyar ta cinye hanyoyi da gadoji, ta kuma katse wadansu al’umma da sauran makwabtansu.

Hakan na faruwa ne yayin da da kasar ta Zimbabwe ta ke kokarin farfadowa daga fari da ta fuskanta na tsawon shekaru biyu da ya rage amfanin gona.

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce a bara kasar Zimbabwe wadda a da, ake mata kirari a matsayin "kwandon abincin Afrika ta kudu," ta na fama da karancin abinci mai gina jiki tsakanin kananan yara, matsalar da ta kasance mafi girma da kasar ta fuskanta cikin shekaru 15.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG