Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliya: Za A Fuskanci Barkewar Kwalara, Rashin Abinci Da Tsaro A Maiduguri -MDD


This aerial view shows houses submerged under water in Maiduguri on September 10, 2024.
This aerial view shows houses submerged under water in Maiduguri on September 10, 2024.

Rahoton da ofishin kula da ayyukan bada agaji na Majalisar Dinkin Duniyar ya fitar, yace abubawan da za’a bukata cikin gaggawa sun hada da abinci da tsaro da wurin kwana da kuma tsaftataccen ruwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da yiyuwar barkewar cutar kwalara a sansanonin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da aka kafa a Maiduguri, babban birnin Borno sakamakon samun rahoton ambaliyar ruwa a jihar.

Rahoton da ofishin kula da ayyukan bada agaji na Majalisar Dinkin Duniyar ya fitar, yace abubawan da za’a bukata cikin gaggawa sun hada da abinci da tsaro da wurin kwana da kuma tsaftataccen ruwa, inda ya kara da cewar wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurbace, kuma na iya janyo barkewar cututtuka irinsu kwalara.

An ruwaito rahoton na cewa, “bukatun gaggawa da ake dasu sun hada da abinci da matsuguni da tsaftataccen ruwan sha, saboda wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurbace. Tsaro na daga cikin muhimman abubuwan damuwa, musamman ga yaran da basa tare da kowa ko suka rabu da danginsu da tsofaffi da masu bukata ta musamman.

Wuraren da ambaliyar tafi shafa a birnin Maiduguri sun hada da Gwange da Hanyar Bama da Gidan Namun Daji da Gidan Waya da Sakatariyar Jihar da Titin Legas da Fadar Shehun Borno da babbar kasuwar Maiduguri da yankunan Custom da Gamboru da Budum da Asibitin Kwararru da kuma gaba dayan yankin gidan waya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG