Ambaliyar ruwan da akan yi a Najeriya da daminar kowace shekara, wannan karon ta kashe mutane sama da 100.
Hotunan talabijin da aka nuna jiya Litini, sun nuna yadda ruwa mai cike da tabo ya kai har tsawon rufin gidaje tamkar kogi, ya na ta malala kan tituna.
Wasu mazuna wuraren sun ce sun tsere ba tare da tunanin kwashe kayan abinci ko wasu kaddarori ba.
Rahotanni na nuna cewa al'amarin ya fi muni a birnin Lokoja, inda kogunan Binwai da Naija su ka hadu. Ambaliyar ruwa ta kashe mutane sama da 350 a 2012 baya ga lalata amfanin gona da sauran kaddarori.
Kwararru kan yanayi sun dora laifin ambaliyar shekara-shekarar kan abin da su ka kira rashin inganta madahun harkokin yau da kullum, ciki har da lambatu da madatsun ruwa da kuma kulawa da wadanda aka gina.
Facebook Forum