Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Almajirai da Yawon Bara

Rashin taimakawa malaman makarantun Islama ya sa suna fita da yaransu zuwa wasu garuruwa inda bayan yaran sun tashi karatu sai su shiga yin bara domin neman abinci

A kasashen Hausa yaran makarantun tsangaya sukan fita yawon bara domin neman abinci da zasu ciyar da kansu.
Baicin ciyar da kansu sukan kaiwa malamansu abun da ya ragu domin su ma su samu su ci.
Sau tari malaman sukan fita da yaran zuwa wasu garuruwa daban inda yaran kan yi bara bayan sun tashi daga makaranta. Babu wuya kuma wasu yaran su shiga wasu halayen da ba na kwarai ba ne. Ana iya yaudararsu su shiga wani hali daban da karatun da suke yi.
Wasu na ganin idan da iyayen yara zasu dinga taimakawa malaman da kudi da abinci suna iya zama wuri guda su koyas da yaran yayinda yaran zasu dinga zuwa makarantun daga gidajen iyayensu.
Dole ne hukumomi a Nijar da arewacin Najeriya su nemi hanyar kawar da barace baracen yara kanana. Misali a kudancin Najeriya Yarbawa da akasarinsu musulmai ne basa bari 'ya'yansu na bara duk da cewa su ma suna karatun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG