Kwararru kan yaki da cutar Ebola suna farin cikin nasarar da aka samu hada allurar da zata yaki Ebola wanda yake da tasiri sosai, duk da haka suna gargadin cewa zai dauki watanni kamin allurar ko maganin su wadata.
Wata gonar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Marie-Paule-kieny ta gayawa manema lbarai cewa allurar rigakafin zata hana barkewar annoba na gaba, amma zai dauki lokaci kamin masu bada izini ko sa ido kan harhada magunguna su amince da allurar tukuna.
Babban jami'in hukumar kiwon lafiya ta duniyar a kasar Guinea Mohammed Benhussien, yace ci gaban da aka samu abun farin ciki ne, duk da haka yace kada jama'a su saki ciki daga matakan hana kamuwa da cutar.