‘Yan majalisu da kafar yada labaran kasar sun ce Chalabi ya rasu ne a birnin Bagadaza yana mai shekaru 71, yayin da ya ke rike da mukamin shugaban kwamitin da ke kula da kudade a majalisar dokokin kasar.
Ya kwashe mafi yawan rayuwarsa ne a kasar Birtaniya da Amurka, inda ya samu digiri na biyu da kuma digirin digirgir.
Mutane da dama na alakanta zamansa a Amurka da mamaye Iraqi da Amurka ta yi, wanda ya yi sanadin hambarar da gwamnatin Saddam Hussein.
Mr. Chalabi shi ne wanda ya baiwa Amurka bayanan sirrin cewa Iraqi na da makaman kare-dangi, sai dai kimarsa ta fadi a idon mutane da dama bayan da aka gano Iraqin ba ta da makaman.