A Somalia kuma, kwamitin alkalai da suka yi shari’a a kan takaddamar zabe sun yi watsi da sakamakon zabukan kujerun majalisu goma sha daya sanadiyar kurakurai da aka gano har da harbin bindiga da aka yi a wata runfar zabe.
Hukunci da kwamitin alkalai masu shari’a a kan lamurran zabe a Somalia, zai iya kawowa zaben shugaban kasa cikas da kasar ke niyar yi a karshen shekara.
Masu sukar lamirin kwamitin sun ce akwai wasu muhimman batutuwan magudin zabe da ba a kula da su ba. Suka ce a cikin batutuwan akwai tsoma baki kai tsaye daga fadar shugaban kasa Hassan Sheikh Mohamoud.
Sai dai shugaba Mohamoud bai mai da martani a kan wannan zargi ba.