Hakan ya biyo bayan rahotannin da ke karuwa na rikicin kasar. A da dai dakarun zasu bar kasar ne a karshen ranar Lahadin gobe, to amma yanzu sai Agusta.
An kada kuri’ar bayan fage ne a Majalisar da ke tsugune a New York ta nan Amurka.
Inda shugabannin ke tunanin kai karin dakarun tsaro ko kuma kakaba takunkumin hana sayen makamai ko ma duk matakan guda biyu akan jaririyar kasar data tuburewa zaman lafiya.
Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power ta bayyana yadda ake samun karuwar rahotannin tashin-tashina a Sudan ta Kudu din.
Wanda har hakan ya sa dimbin jama’a sun bazama sansanonin sojojin kiyaye zaman lafiya don neman mafaka.