Ana bukatar hadin kan dukan kananan hukumomin Najeriya 774 kafin a iya cimma burin shawo kan cutar shan inna.
Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido da ministan lafiya Dr. Onyebuchi Chukwu da kuma karamin ministan lafiya wanda shine shugaban kwamitin shugaban kasa na musamman kan yaki da cutar shan inna, Dr. Muhammed Pate ne suka bayyana haka a Abuja bayan zaman kwamitin a fadar shugaban kasa.
Sun bayyanawa shugaban kasa Goodluck Jonathan, cewa kananan hukumomi 34 suna kawo cikas a wannan yunkurin kasancewa basu taka rawar gani wajen daukar matakan yaki da cutar ba.
A cikin jawabinshi, shugaban kwamitin shugaban kasar Dr. Pate, yace duk da yake ana kokarin rage raduwar cutar, ba a shawo kanta baki daya ba. Ya bayyana cewa,an sami kanananan yara 49 da cutar a kananan hukumomi 34 na jihohi goma na kasar inda aka sami kashi 50% na masu dauke da cutar a jihohin Katsina, Kaduna da kuma Kano. Yayinda rahoton ya nuna cewa, ba a sami bullar cutar ba a jihohi 24 cikin shekaru biyu. Bisa ga cewarshi, kananan hukumomi biyar ne kadai a kasar suke kawo cikas a cimma burin shawon kan cutar.
Wadanda suka halarci zaman sun hada da gwamnoni da wakilan Hukumar lafiya ta Duniya da asusun tallafawa kananan yara UNICEF da kuma gidauniyar Bill da Milinda Gates.