Babbar jam’iyyar hamayya a Liberia ta kauracewa zaben na shugaban kasar Liberia bisa zargin yin magudi. Tsohon ministan shari’a Winston Tubman, wanda yake kalubalantar shugaba Ellen Johnson a zaben na ranar Talata, shi yayi kira ga magoya bayansa da su kauracewa zaben, ganin cewa an shirya yin magudin da zai baiwa Shugaba Sirleaf nasara.
An karfafa daukan matakan tsaro a binrin Monrovia, musamman a kewayen shelkwatar Mr. Tubman na jam’iyyar CDC, inda zanga zangar da ‘yan hamayya keyi ke haduwa da martanin ‘yan sanda, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.Wakilin muryar Amurka a Liberia yace masu kada kuri’a basu fito sosai ba harma a rumfunan da aka saba cika, jami’an tsaro a daren jiya suka rufe gidajen radio uku ciki har da gidan Rediyon Mr. George Weah, dan takarar mataimakin shugaban kasa Mr. Tubman.