Yayinda kungiyar Ecowas ke kokarin daukar matakin soja domin kawarda shugaban kasar Gambia, mai barin gado Yahya Jammeh, daga mulki domin maye gurbinsa da Adama Baro, wanda hukumar zaben kasar ta bayyana a mtasayin wanda ya yi nasara.
Masu nazari akan al’amurn yau da kullum na ganin hanyar tantaunawa ta diflomasiya, mataki mafi dacewa domin kaucewa barkewar wani sabon rikici a yankin da ke fama da matsalar ta’addanci.
Tun da shugaba Jammeh, ya amince da sakamakon zaben na kasar Gambia, shugaban kasar Nijar, Issoufu Muhammadou, ya aikawa sabon shugaban sakon taya murna.
Wannan na nufin cewa kasar Nijar, bata laminci watsin da shugaba mai barin gado Yahya Jammeh, yayi da wanna sakamako ba wanda har yasa kungiyar Ecowas shirye shiryen kawar dashi daga mulki, baya shudewar wa’adinsa ranar 19, ga watan Janairu, na sabuwar shekara, ta hanyar amfani da karfin Soja.
AlKassim Abdulrahaman, wani mai sharhi akan al’amuran yau da kullum, yace akwai hadari sosai amma hanya mafi kyau itace ta sasantawa, abinda yakamata a tuna shi cewa amincewar dashi shugaban kasar yayi da kuma daga bisani ya kai kara Kotu toh amincewa ko watsi da kara shine abinda zai taimaka wajan warware matsalar da ake ciki.