A wannan zamanin abu ne mai wuya ka ga wani wasan bidiyo gem da aka yi da ‘yan wasa daga cikin fitattun 'yan Afrika, da yawa sai dai ka ga wasu mutane da su ka yi fice a fadin duniya. Ko me ya kawo hakan.?
Akwai bukatar kasashen Afurka su tashi tsaye wajen bunkasawa da kuma kirkiro wasannin bidiyo gem, musamman wajen amfani da wasu shahararru ko gwaraza da suka taka muhimmiyar rawa a nahiyar a matsayin ‘yan wasan.
Ta haka ne kawai matasa a nahiyar zasu dinga alakanta kansu da wadannan mutane da kuma kokarin zama kamar su, haka akwai bukatar shigo da al’adu, harsuna, sutura da dai duk wasu abubuwa da zasu dinga nuna cikakkiyar rayuwar kasashen Afurka.
Wani kamfanin kasar Canada na hada hannu da kamfanin shirya wasan bidiyo gem a kasar Kenya don farfado da kasuwancin a nahiyar.
Abun tambaya a nan shi ne “Wai yaushe kuka ga wani wasan bidiyo gem da aka yi shi, kuma ‘yan wasan suka wakilci wani jarumin kasashen Afurka?” Lokaci ya yi da ya kamata a dinga yin wasannin bidiyo game na Afrika don ‘yan Afurka, da samar da yanayin Afurka.
Wanda a duk lokacin da matasa suka buga gem din, zasu dinga ganin kansu a ciki, ba tare da juya musu tunanin su irin na wasu al’adu da ba na kasashe daban ba.
Facebook Forum