Ado Ahmad Gidan Dabino -- Duk da cewar fim dina na Juyin Mulki bai samu damar shiga gurbin fina-finan da aka zaba a gasar fim na FESPACO da aka gudanar a kasar Burkina Faso, hakan bai karya min gwiwa ba, domin kuwa ire-iren wadannan taron ne da ke baiwa jarumi damar samun shiga jerin fina-finan duniya.
Gasar Fespaco wato kalankuwar fina-finai ta Africa wanda aka gudanar a Burkina Faso, wadda ya shiga gasar ne ta shafin internet inda ya cike bayanansa, ya kuma aika da fim din mai suna a Juyin Sarauta.
Hakan yasa na ga cancantar biya wa kai na kudin domin na hallarci taron na mako guda, tare da samun ilimi da zai sa fina-finai na su shiga tsara, baya ga haduwa da wasu masu shirya fina-finai na wasu kasashen daban daban.
Gidan Dabino ya ce hanya ce ta inganta ilimi da samun wasu dabaru na bunkasa sana’ar fim, sannan ya kara da cewa kashi casa’in cikin dari kasashen da ke harshen Faransanci ne suka mamaye taron.
Amma wani abun sha’awa kuwa kasar Rwanda ce ta lashe gasar, wacce kuwa harshen Turanci ne harshe da kasar ke afani da shi, Ado Gidan Dabino, ya kara da cewa a yanzu ya samu wasu dabarun da zai yi amfani da su, idan zai shiga da fim din sa cikin wannan kasa a shekaru biyu masu zuwa.
Facebook Forum