Shugaban kwamitin kulawa da 'yan gudun hijira Alhaji Sani Zoro ya shaidawa manema labarai cewa akwai bukatar a kai agajin gaggawa wa duk sansanin 'yan gudun hijira dake kasar.
Shugaban yayi furucin ne lokacin da ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira dake garin Dambua cikin jihar Borno tare da sauran 'yan kwamitinsa. Sun kai ziyar ce da zummar gani da idanunsu halin da 'yan gudun hijiran ke ciki.
Alhaji Sani Zoro yace sun fahimci cewa akwai matsaloli da dama da 'yan gudun hijiran ke fuskanta, musamman wadanda ake fito dasu kwana kwanan nan da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa dasu sakamakon irin halin da suka shiga na tsanancin yunwa. Alkamumma da suka fito daga baya sun
nuna cewa yara fiye da dubu hamsin ne suke fama da karancin abinci. Irin wadannan yaran suna bukatar tallafin gaggawa. Alhaji Zoro yace idan ba'a kawo agajin gaggawa ba yaran na iya mutuwa.
Alhaji Zoro ya bayyanawa Muryar Amurka irin matsalolin da yace sun gano da kuma matakan da ya kamata a dauka nan take. Akwai bukatar a karo magunguna da abinci cikin gaggawa. Akwai wasu mutane kimanin miliyan biyu da har yanzu suna hannun 'yan Boko Haram. Yaki bai kai wurinsu ba saboda haka yakamata a soma yin tanadi kafin a kubutar dasu. Idan ba'a yi haka ba suna fitowa matsalolin abinci da wurin tsugunawa zasu tsananta. Yanzu akwa rashin lafiya da rashin asibitoci da rashin makarantu saboda haka akwai bukatu kwarai da gaske. Yanzu ma akwai mutane fiye da dubu dari biyu da hamsin dake bukatar abinci da wurin kwanciya da magani da ruwa da kuma abubuwan da zasu inganta lafiyarsu.
Wasu 'yan gudun hijiran da aka zanta dasu a garin Dambua sun yi korafi akan rashin abinci da magani da kuma yawan mutuwar yara. Wasu 'yan gudun hijiran daga Kamaru da Chadi sun ce an hanasu tallafin abinci sai dai su shiga daji su tsinko yakuwa su ci. Wata matsalar da ka iya haddasa annobar cuta ita ce ta rashin wajen zagayawa domin yin tsuguno. Runfunan da aka yi masu idan an yi ruwa suna jikewa.
Ga karin bayani.