Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Alamomin Tambayoyi kan Tsarin Tsaro a Arewa


Matasa
Matasa

Ganin yadda wasu rahotanni ke cewa akwai sojojin Najeriya tare da kungiyar Boko Haram da yadda aka ce jirage masu saukan anugulu na kaima 'yan ta'ada kayan aiki ya sa matasan arewa da daliban arewa suka yi taro a Kaduna inda suka kalubali tsarin tsaro a arewa.

Kungiyoyin dalibai da matasan arewa sun yi wani gangami a Kaduna inda suka ce akwai alamamomin tambaya a tsarin tsaro cikin arewacin Najeriya.

Taron ya tashi da cewa akwai lauje cikin nadi kan tsarin tsaro a arewa. Lamarin sun ce tamkar an mayarda 'yan arewa wawaye ne. Dr Usman Bugaje wanda ya yi jawabi a wurin taron yace mutanen da suke ta kashe 'yan arewa jirage masu tashin angulu ke kawo masu makamai da abinci. Tambaya nan ita ce daga ina jiragen suka fito. An ce wai Fulani ne to daga ina Fulanin suka fito da jirgi? Yace an mayarda 'yan arewa wawaye domin shugabannin yankin arewa sun kasa yin wani abu domin abun da suke samu a gindin gwamnati.

Shi ma Barrister Solomon Dalung wanda ya halarci taron yace akwai shakku game da hare-haren da ake kaiwa a wasu sassan arewa. Yace an ce Fulani ne amma ai shanu aka san Fulani da su ba jirgi mai tashin angulu ba. Yace watakila Fulanin gwamnati ne. Idan jirgi na yawo a kasar bada sanin gwamnati ba me ya sa ba'a harboshi ba. Yace an barsu suna yawo suna kashe mutane. Sun kashe a Makurdi. Sun kashe mutane a Filato. Jirgin sama ya sauka ya kashe mutane a Katsina.

Barrister Dalung yace wadanda aka rutsa dasu suka kawo batun jirgi. Yace wani abokinsa 'yan Boko Haram sun tsaresu suna kwance a kasa ana ta kashe-kashe kafin a kawo kansu.Can sai wani jirgi ya zo ya sauka inda suke 'yan Boko Haram suka barsu suka je suna karban abinci da makamai sai shi kuma wanda aka tsare ya samu hanya ya gudu. Mutumin ne ya kawo bayyanin jirgin sama. A Katsina mutane sun hango jirgi mai saukan angulu yana sauka lokacin da aka kai hari. Harin da aka kai garin Paul Unongo a Binuwai jirgin sama ya sauka a wurin.

Alhaji Ashiru Sheriff shugaban kwamitin amintattu na kugiyar matasan arewa yace tun da aka soma rigingimun nan da aka soma a Filato, Kaduna, Borno,Adamawa, Yobe, Binuwai, Nasarawa da sauran wuraren shugabannin arewa basu zauna sun ce bari su nemarma arewa mafita ba. Manya irin su T.Y. Danjuma, IBB da su Buhari basu taba haduwa sun ce zasu yi wani abu ba. Wadannan manyan da ma wasu ire-irensu basu taba fitowa ba su ce basu yadda da abubuwan dake faruwa ba.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG