Wannan wani labari ne mai ban tausayi na wani tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafar kasar Ghana, 'Ghana Black Stars' Abubakari Garba wanda ake ma lakabi “Goal Na Mefife” da ya tada hankalin masu sha’awar kwallon kafa a Ghana, bayan ya ba da labarinsa, sai ya yi bara kafin ya ci abinci duk da irin sadaukar da rayuwarsa da ya yiwa kasar.
Abubakari ya fada a cikin wani hoton bidiyo da abokin aikin mu Baba Yaku Makeri ya yi mana sharhi, ana masa lakabi da Goal Na mefife da harshen Ashanti, ma’anar lakabin da Hausa shine, ina neman zura kwallo ne, saboda yunwar saka kwallo a raga a duk lokacin da yake wasa.
Ya fada a cikin bidiyon cewa ya yiwa kungiyarsa ta Asante Kotoko da kasarsa bauta, amma babu wani amfani da ya samu, a wasannin da ya yiwa Kotoko da wasu kungiyoyin kasashen waje.
Ya ce "ni dan wasan gaba ne, ina gudu sosai kuma ina iya tserewa abokan karawa, ina iya harba kwallo tun daga tazara mai nisa kuma in zura kwallo a raga, saboda ina sha’awar haka.
Ya kara da cewar "ba zaka iya dauka kofi idan baka zura kwallo a raga ba, sai dai yace ba zai iya tuna adadin kwallaye da ya zura ba. Na fara wasa na ne daga garin Tamale kafin naje kungiyar Kotoko inji Abubakari. Na kuma yiwa Black Stars wasa a gida da waje amma babu wani amfani, na yiwa kasa bauta amma yanzu sai nayi roko kafin naci abinci”
Akwai kuma wani tsohon gola da ya yiwa Ghana da Accra Hearts of Oak wasa, Ali Jarrah, wanda shi kuma ya bayyana bakin cikinsa a kan yanda shugabannin hukumomin kwallon kafa suke barin gwarzayen kasar suke mutuwa cikin bakin ciki da damuwa, duk da irin gudunmuwar da suka bayar wurin daga tutar Ghana sama a idon duniya.
Shi ma dai yace yana cikin damuwa tun lokacin da ciwon mutuwar bangare jiki ya kama shi, shekaru 25 da suka shude, lamarin da yasa aka yi watsi da rayuwarsa, sai ya sha wahala kafin ya samu abin da zai kula da rayuwarsa, alhali kuwa a wasu kasashen duniya kasar ce zata dauki dawainiyarsu.
Facebook Forum