Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana-Akalla Mutane 6 Ne Suka Halaka Sakamakon Wata Fashewa A Tashar Iskar Gas


'Yan kwana-kwana a inda fashewa ta auku a daren Asabar.
'Yan kwana-kwana a inda fashewa ta auku a daren Asabar.

Fashewar ta tilastawa mazauna gudu daga gidajensu, karar da aka ji a duk fadin Accra.

Rahotanni daga Ghana sun ce akalla mutane shida ne suka halaka, wasu fiye da 35 kuma suka jikkata bayan da wata tashar iskar Gas tayi bindiga a wuri da ake kira Atomic Junction, kusa da kauyen da ake kira Legon dake arewa maso yammacin Accra, babban birnin kasar, kamar yadda hukumar kashe gobara ta kasar.
Fashewar da ta auku a atashar ta tilastawa mazauna yankin gudu daga gidajensu a daren jiya Asabar, saboda karfin fashewar anji kararta a duk fadin birnin, kuma ta haddasa wuta mai girman gaske.

Shugaba Nana Akufo-Addo ya bayyana alhini da kuma yin ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su. Yayi addu'ar Allah ya baiwa wadanda suka jikkata sauki cikin hanzari.

Tuni shugabn kasar ya tura mataimakinsa Muhammadu Bawumia ya ziyarci inda fashewar ta auku a yau lahadi. Ya kara d a cewa a shirye gwamnati take ta dauki matakin ganin haka bai sake aukuwa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG