Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 19 Suka Rasa Rayukansu a Libya


Masu ceto suke kokarin kawar da wadanda suka jikata zuwa asibiti a Libya
Masu ceto suke kokarin kawar da wadanda suka jikata zuwa asibiti a Libya

Sakamakon arangama tsakanin mayakan sa kai na kungiyoyi masu gaba da juna an samu asarar rayuka a Libya

A kalla mutane 19 ne suka rasa rayukansu biyo bayan arangama jiya Alhamis tsakanin mayakan sa kai na kungiyoyin dake gaba da juna a gabashin Libiya, sannan kuma wata motar daukar mai ta kama da wuta a wasu rigingimun na daban.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa ne yace duka mutane 19 da suka rasa rayukansu a kusa da birnin Sirte sojoji ne.

A wani lamarin na daban kuma an harba roka akan wani wajen ajiye mai a garin Es Sider, inda rahotanni suka nuna cewa an samu gobara, amma jami’ai sunce barnar da aka samu ba mai yawa bace.

Gwamnatin Libiya da gwamnatocin kasa da kasa suka amince da shi. Yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira a gabashin kasar biyo bayan mamayen da ‘yan tawaye suka yiwa wasu bangarorin babban birnin Tripoli tun watan Agusta.

A farkon wannan makon ne, Majalisar Dinkin Duniya ta bada rahoton cewa rigingimun Libiya sun kashe daruruwan fararen hula tun watan Agusta, kuma ana zargin wasu kungiyoyin mayaka a kasar da laifukan keta hakkin bil adama.

XS
SM
MD
LG