Kungiyar kwallon kafa ta Ajax ta lashe Kofin gasar kwallon kafa na kasar Holland a karo na 34 jiya Laraba 15 ga watan Mayu, bayan da ta yi nasara akan kungiyar De Graafschap da ci 4-1, mako daya bayan da kungiyar Tottenham Hotspur ta yi waje da ita a gasar zakarun turai.
kwallayen da 'yan wasa Lasse Schoene, Nicolas Tagliafico da Dusan Tadic suka ci, bayan hutun rabin lokaci, sun bai wa kungiyar da Erik ten Hag ke jagoranta nasara a karo na 8, sannan suka lashe kofin gasar a karshen mako.
Kungiyar kwallon kafa ta Ajax ta je wasan karshe na wannan kakar wasanin, bayan da ta bai wa abokiyar hamayyar ta PSV Eindhoven tazarar maki uku da banbancin kwallaye 14, a lokacin da ta lallasa Utrecht da ci 4-1, sannan masu rike da kofin suka sha kaye da ci 1-0, a hannun AZ Alkmaar a ranar Lahadi.
Bazar da suka nuna a gasar cin kofin nahiyar turai, wacce ta ba su damar yin waje rot da kungiyar Juventus ta Cristiano Ronaldo ta zo karshe a wani irin yanayi, bayan kwallon da Lucas Moura ya aika cikin minti 96, ta sa Ajax ta zubar da damar jumillar kwallaye uku da ta ba da tazara, sannan ta sa ta gaza samun damar zuwa Madrid.
Facebook Forum