Aisha Falke wata mai sana’ar dinki wacce ta shafe shekaru kimanin 11 ta na wannan sana’a ta dogaro da kai, kuma a hannu guda marubuciya ce a kafofin sadarwar zamani.
Aisha ta ce tana dinkin kayan mata musamman ma dunkunan dangogin dogayen riguna na mata da sauran su, bayan ta gama yi wa kasa hidima ne ta yi tunani cewar aikin gwamnati ba nata bane.
Daga cikin irin kalubalen da ta ke fuskanta ta ce akwai matsala ta rashin samun wadatacciyar wutar lantarki, da matsala ta ma’aikata, inda ta ce a mafi yawan lokuta sai ta koyawa mutane aiki, sun iya sosai sai kwatsam suce zasu bar aikin.
Babban burin ta a cikin sana’a ta shine na zama babbar dila da za’a dinga zuwa wajen ta, ana saran kaya ana sayarwa a wasu wurare, kuma ta kara da cewa a yanzu tana da mutane kimanin 10 a karkashinta da su ke aiki.
Sannan ta ce burinta dai ta zama ana zuwa daga jihohi daban daban ana sarar kayayyakinta domin sayarwa a sauran sassan kasar nan.
Facebook Forum