Batun kiwon lafiya shi ne na uku a jerin dawwamammun muradun raya kasashe 17 da ake so a cimma nan da shekara ta 2030, wanda ya yi daidai da wannan shiri da uwargidan shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta kaddamar a karkashin wakilicin matar mataimakin shugaban kasa, Mrs Dolapo Osinbajo.
Hajiya Hajo Sani, mai ba da shawara ce ta musamman a ofishin uwargida Aisha Muhammadu Buhari, ta kuma yi karin bayani kan wannan shiri na inganta lafiyar mata masu juna biyu da na kananan yara.
A lokacin gabatar da nata jawabin a gaban taron, uwargidan shugaban majalisar dattawan Najeriya Toyin Saraki wacce itama ta halarci taron ta ce batun lafiyar mata masu juna biyu, batu ne da ke zukatan kowa da kowa.
"Ta ce maida hankali kan abinda ya shafi harkar kiwon lafiya, abu ne da ke zuciyar uwargada Aisha Buhari, na kuma yi imanin cewa abu ne da duk ‘yan Najeriya ke da muradi akai."
Uwargidan gwamnan Jahar Edo, Lara Adams Oshiomole, ita ce ta wakilici matan gwamnonin jihohun Najeriya 36. Yayin nata jawabin ta ce yana da matukar muhimmanci da aka maida hankali kan wannan batutuwa da suka shafi mata masu juna biyu a daidai wannan lokaci.
Yankin Arewa Maso gabashin Najeriya dai , shi ne yankin da kididdiga ta nuna cewa an fi samun yawaitar macemacen mata masu juna biyu da yawan mace macen yara ‘yan kasa da shekaru biyar, a cewar Sanata Binta Masi Garba da ke wakiltar mazabar arewacin Adamawa.
Tun ba a yau ba, Najeriya ta dade tana fuskantar matsaloli da dama a fannin kiwon lafiya, musamman a fannin yawaitar macemcen mata masu juna biyu da yara ‘yan kasa da shekaru biyar, ko menene ya sa hakan?
Dr Ado Muhammed shi ne shugaban hukumar da ke kula da kiwon lafiya a matakin farko a Najeriya, ya kuma halarci wannan taro
Ko yaya kungiyoyin fararen hula ke kallon wannan shiri, Dr. Muhammed Lecky shi ne shugaban kungiyar da ke sa ido kan harkokin kiwon lafiya a Najeriya.
Y ace wannan ba wai sabon abu ba ne, sai dai abin da mu ke gani anan shi ne an samu bangaren masu fada aji sun sa baki kan harkokin da suka shafi mace macen mata masu juna biyu da samar da abinci mai gina jiki da kula da lafiyan yara kanana.
A karshen wannan taro duk bangarorin da suka halarta sun sha alwashin za su dauki matakan da suka rataya a wuyansu domin ganin wannan shimfida da aka yi ta samu nasara.
Ga rahoton Mahmud Lalo.