Hatta gwamnan jihar Neja Dr Muazu Babangida Aliyu ya koka game da yadda akin bada katin zaben ke gudana a lokacin da ya je majalisar dokokin jihar domin mika kasafin kudin jihar na shekara mai zuwa.
Yace a cikin kananan hukumomi guda ashirin da biyar na guda goma sha daya aka kawo. Cikin goma sha dayan ma babu inda aka samu daidai. A kowane wuri za'a tarar cewa wadansu da aka yiwa rajista basu samu ba. Ban da haka da an ce idan ba'a samu sunan mutum ba za'a sake yi masa rajista. Gwamnan yace naurorin da aka kawo da yaran dake yin aikin dukansu babu abun kirki cikinsu. Yace yayi magana da shugaban hukumar zaben ta INEC kuma ya tabbatarmasa komi zai yi daidai.
Gwamnan ya kira INEC da majalisun tarayya su san can cewa babu yadda za'a yi zabe idan har sun dage kan dole sai an yi anfani da katin zabe na din din din. Dole su fito da wata hanya yadda duk wanda aka yi ma rajista a barshi yayi zabe.
Majalisar dokokin jihar tace tana shirin daukar mataki akan lamarin. Adamu Usman shugaban majalisar dokokin yace zasu baza 'yan majalisar zuwa mazabunsu su tattaro bayanan abubuwan dake faruwa kafin su tsayar da kudurin cewa a bar mutane su yi anfani da tsoffin katukansu. Yace koina aka je akwai matsaloli.
Tuni jam'iyyar APC tace a ma dakatar da bada katin zaben domin bata gamsu da yadda lamarin ke tafiya ba. Shugaban APC a jihar Injiniya Muhammad Inuwa yace sun nemi a dakatar da aikin domin suna son a yi adalci.
Amma hukumar zabe tace ta sha karo da wasu matsaloli ne amma yanzu ta shawo kansu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.