An dai kama su da kudi fiye da miliyon daya da ma wasu motoci guda hudu, da bindiga kirar AK 47 guda biyar da kuma wasu bindingoji kirar hannu guda 21.
SP Sulaiman Yaya Nguroje shi ne kakakin rundunar yan sandan jihar ta Adamawan wanda ya yi mana karin haske dangane da wadanda ake zargi da manyan laifuffuka a jihar, irin su garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da satar shanu. Ya ce an kama mutane 30 inda aka kwace bindigoji da kudi a hannunsu.
Aliyu Muhammad na daya daga cikin wadanda ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Adamawa, wanda rundunar 'yan sandan suka kama ya ce wannan shi ne karon farko da ya fara wannan mugun aiki na garkuwa da mutane amma kuma sai gashi yan sandan sun kama shi.
A hirarsa da Muryar Amurka, Aliyu Buba daga karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa wanda ya ce sau uku yana yin garkuwa da mutane a yankin Mayo Ballwa da kuma karamar hukumar Yola ta Kudu suna karbar kudi amma su basa samun wani abin kirki.
Shi ma Ibrahim Adamu, yana cikin wadanda ake zargin, sai dai ya ce shekaru biyu kenan da barin sa wannan mummunan aiki sai ga shi kuma yan sandan sun kama shi, amma ya taba yin garkuwa da mutane sau biyu a baya, amma ya bari yanzu.
Saurari rahoton Lado Salisu Garba:
Dandalin Mu Tattauna