Malaman makarantun sankandare su fiye da dari shida sun kwashe fiye da shekaru uku suna koyaswa ba tare da biyansu ko kwandala ba.
Majalisar dokoki da kungiyar kwadago duk sun shiga tsakani amma batun ya cutura lamarin da ya tunzurasu shekawa kotun sauraren karakin kwadago saboda neman hakkinsu.
Mr. Fredrick Mbashi jagoran malaman yace dole ya sa suka garzaya kotu saboda neman hakkinsu ganin cewa duk wani kokari da suka yi bai samu nasara ba. Yanzu suna cikin mawuyacin hali na kuncin rayuwa.
Wasu cikinsu, a cikin mawuyacin halin sun rasa rayukansu. Wasu matansu sun rabu dasu. Wasu sun rasa gidajen haya da suke ciki saboda basu iya biyan kudin haya ba.
Shugaban kungiyar lauyoyi na jihar Barrister Abubakar Baba Kano wanda shi ne lauyan malaman yace idan gwamnati bata son ta daukesu aiki ta biya kudin watanni 19 da suka yimata aiki.
Kwanakin baya shugaban kungiyar kwadago Dauda Maina ya kawo batun gaban gwamnan jihar Sanata Muhammadu Bindo. Gwamnatin ta gaji matsalar ce daga tsohuwar gwamnatin da ta shude.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.