Kwamishinyar ta furta haka lokacin da take bayanin ko gaskiya ne an sauyawa likitan da ya aiwatar da fidar wurin aiki zuwa karamar hukumar Maiha da batun sake bude asibitin da aka rufe kwanan baya.
Bincike ya nuna yanzu haka an sauyawa majinyaci inda yake jinya a asibitin Aminu Kano zuwa asibitin gwamnatin tarayya dake Gombe sakamakon yajin aikin da ma’aikatan jinyar suka shiga kamar yadda wani daga cikin danginsa Malam Umaru ya shaida inda yake bayanin matsalarsu yanzu itace ta karancin kudi koda kuwa kodar ta samu.
Dalilin haka ya sa majalisar dokoki ta jihar Adamawa ta yi alkawarin sadaukar da wani kaso na albashinsu na watan Maris don tallafawa Isa Hamman kamar yadda jami’in hulda da jama’a na majalisar Yahaya Mohammed Daji ya bayyanawa Muryar Amurka.
Ga bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum