Kwamishanan labaran hukumar alhazan Najeriya Dr Saleh Okenwa shi ya bayyana karin adadin wadanda suka rasa rayukansu a turmutsistin Saudiya.
Yanzu sun kai dari da arba'in da biyar, wato sun tashi daga tasa'in da tara na alkaluman baya. Har yanzu kuma ana kokarin gano ko tantance mutane 165 da ba'a san inda suke ba ko kuma abun da ya faru dasu.
Shugaban hukumar Alhazan Barrister Abdullahi Muhammad Mukhtar a jawabinsa ya musanta wani bidiyo da ake yayatawa dake nuni da cewa ba'a mutunta gawarwakin wadanda suka mutu ba.
Shugaban yace hukumar tana nan tana bin alkawarin da sarki Salman ya yiwa wadanda naurar gini ta kashesu a masallacin Ka'aba. Ofishin jakadancin Najeriya dake Jeddah zai tabbatar ya karbo ma mutanen hakinsu.
Ga karin bayani.