Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Najeriya Ya Zarta 21,000


Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19.

A cewar hukumar, mutum 452 ne cutar ta harba wanda hakan ya mayar da gaba dayan adadin zuwa 21,371.

Daga jihohi 19 na kasar aka samu sabbin alkaluman, kuma har yanzu jihar Lagos ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar wadda coronavirus ke janyowa, inda yanzu ta sake samun mutum 288. Sai jihar Oyo da ke bin ta da mutum 76.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Rivers inda aka samu mutum 56, 31 a Delta, 30 a Ebonyi, 28 a Gombe, 20 a Ondo, 20 a Kaduna, 20 a Kwara, 17 a Ogun, 16 a birnin tarayya Abuja, 13 a Edo, 10 a Abia, 9 a Nasarawa, 9 a Imo, 8 a Bayelsa, 8 a Borno, 8 a Katsina, 3 a Sokoto, 3 a Bauchi, 2 a Plateaeu.

A sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter a daren ranar Talata 23 ga watan Yuni, ta kuma bayyana cewa mutum 7,338 suka warke daga cutar yayin da mutum 533 suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG