Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19.
A cewar hukumar, mutum 436 ne cutar ta harba wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 20,244.
An samu sabbin alkaluman da aka samu daga jihohi 19 ne, har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar wadda coronavirus ke janyowa, inda yanzu ta sake samun mutum 169. Sai jihar Oyo da ke bin ta da mutum 52.
Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Plateau inda aka samu 31, 29 a Imo, 28 a Kaduna, 23 a Ogun, 18 a birnin tarayya Abuja, 17 a Enugu, 17 a Bauchi, 14 a Bayelsa, 8 a River, 6 a Osun, 6 a Kano, 5 a Edo, 5 a Benue, 3 a Adamawa, 2 a Borno, 1 a Abia, 1 a Ekiti.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 6,879 suka warke daga cutar yayin da mutum 518 suka mutu a jihohi 35, ciki har da birnin tarayya Abuja.
Facebook Forum