Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19.
A cewar hukumar, mutum 575 ne cutar ta harba a yinin jiya Litinin wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 29,286.
An samu sabbin alkaluman da aka samu daga jihohi 19 ne, har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar wadda coronavirus ke janyowa, inda yanzu ta sake samun mutum 123. Sai birnin tarayya Abuja da ke bin ta da mutum 100.
Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Delta-58, Edo-52, Ogun-42, Katsina-24, Bayelsa-23, Rivers-22, Borno-19, Plateau-18, Ondo-18 ,Oyo-17, Kwara-15, Osun-13, Enugu-9, Nasarawa-7, Abia-6, Cross River-5, Kaduna-3, Ekiti-1.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 11,828 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 654 suka mutu.
Facebook Forum