Taron wanda ya hada masu ruwa da tsaki daga bangagori da dama a fadin kasar ya tabo batutuwa da ke ciwa al’ummar Najeriya Tuwo a kwarya musamman ta fuskar tsaro da ke zama barazana ga zamantakewa, da kuma hanyoyin magance matsalar.
Fasto Osari Daniels shi ke zama shugaban kungiyar ta NATIONAL PEACE AND UNITY CAMPAIGN, ya kuma ce "taron zai taimaka wajen sanya kishin kasa a zukatanmu da kaunar juna a matsayin yan’uwa ba abokan gaba ba kuma ba tare da la’akari da inda muka fito ba, za mu iya hada kai wajen ciyar da kasar mu gaba. Dalilin haka yasa muka hadu don wayarwa juna kai, muna da tabbacin cewa idan a na yawan irin wannan ganawar za’a samu maslaha a halin da kasar ta tsinci kanta a ciki’’.
A nashi bangaren, Alhaji Ibrahim Jega tsohon sakataren gudanarwa na babban masallacin Abuja ya ja hankalin yan siyasa da su guji nuna son rai da ka iya tada tarzoma a kwadayinsu na son Mulki.
Shi kuwa Sanata Yusuf Abubakar Yusuf da ke wakiltar jihar Taraba ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya ya bayyana cewa akwai rashin ilimi da fahimta wajen daura laifi ga wata kabila idan rikici ya barke a wani yanki na kasa
Taken taron dai shine ‘’zaman lafiya a Najeriya abu mai yiwa’’ wanda hakan kuwa shine burin duk wani dan’Najeriya mai kishin kasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: