Masana harkokin tsaro na cewa rugujewar gwamnatin Gadhafi a Libya da kungiyar ISIS a Iraqi da Syria su ne suke haddasa barazanar tsaro a kasashen yammacin Afirka.
Babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana matakan da suke dauka a matsayin shawo kan lamarin. Ya ce ita kungiyar ISIS ta hada kai da kungiyar Boko Haram saboda haka suna yaki dasu ne a arewa maso gabashin kasar tare da samun goyon bayan kasashen dake makwaftaka da Najeriya irinsu Chadi da Kamaru da Nijar.
Dangane da alakar dake akwai akan rushewar ISIS da tarzomar kasar Mali da Najeriya, tsohon kwamandan rundunar soji ta bakwai Manjo Janar A.S.Bindawa ya ce idan aka lura, rikicin ya samo asali ne daga gabashin Afirka ya kwararo ta Chadi har ya isa Najeriya. Injish an dade makamai na shigowa kasar babu wanda ya kula ya duba yaya makaman ke shigowa domin a dauki matakin dakile ko kuma toshe duk wata hanya. Sai da tafiya ta yi nisa.
Shi ma babban kwamandan rundunar sojojin Amurka dake Afirka Janar McConville da aka tambayeshi irin taimakon da kasarsa zata baiwa Najeriya cewa yayi kasarsa ta fi ba kawayenta goyon baya akan yadda zasu magance matsalar tsaronsu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum