A yau ne aka shiga rana ta biyu a cikin watan ramadan a duk fadin duniya, wanda musulamai suke gudanarwa duk shekara.
Malam Hamisu Nasid Ibrahim, shi ne limamin masallacin zone 4 plaza da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ya kuma yi karin bayani dangane da ire-iren ibadun da musulmi ya kamata ya yi a watan Ramadana, inda ya fara da cewa, Ramadana wata ne mai albarka da rahama kuma wata ne da ake kulle kofofin wuta gaba dayan su a kuma bude dukkan kofofin aljanna gaba dayan su babu wacce za’a kulle.
Haka kuma ana daure dukkanni shaidanu gaba dayan su, sannan ya ce Allah (SWA) ya na aiko da mala’iku suna shelar ina mai nufin alkhairi ya kusanto.
Malam Hamisu ya ce ubangiji na cewa dukkanin ibadar Allah da mutum zai aikata nasa ne amma azumi na Allah ne, don haka ne ake jan hankalin musulmai da su mai da hankali wajen gudanar da ibadun alkhairi da yawaita karatun alqur’ani da kyautata wa al’umma.
Sai dai kuma ya kara da cewa yana da kyau a yawaita kyauta da farantawa mutane zukatansu da kuma kame harshe da idanuwa da yin sauran ayyukan mutanan kwarai.
Facebook Forum