Wannan na zuwa ne sakamakon yanayin da ake tafiyar da siyasa a kasar musamman a bangaren wa’adin mulkin da ‘yan takarar manyan jam’iyyun kasar biyu zasu yi, cancantar ‘yan takara, tanadin dokar zaben shekarar 2022 da aka yiwa gyarar fuska a kan gudanar da zabe mai zuwa da dai sauransu.
Rudanin da ‘yan kasar suka shiga dai baya rasa nasaba da sakamakon zaben fidda ‘yan takara a dukkan matakai musamman ma ‘yan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki, jam’iyyar adawa ta PDP da sauran jam’iyyu kamar su NNPP, YPP, Labour party da dai sauransu.
Masana siyasa kamar Malami a tsangayar koyar da kimiyyar siyasa a jami’ar gwamnati dake birnin tarayya Abuja, Dakta Abubakar Kari, ya yi bayani a game da Dabi’un ‘yan siyasa a daidai wannan lokaci inda ya ce zai daganta lamarin da karin maganar da hausawa ke cewa 'in ta ruwa rijiya, in bata yi ba, masai', kuma hakan ba daidai ba ne.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yamatu Deba na jihar Gombe a tarayyar Najeriya, Alh. Yunusa Abubakar Ahmed, kira ya yiwa ‘yan kasa su bada karfi wajen fahimtar tanade-tanaden dokar zabe ta shekarar 2022.
‘Yan Najeriya dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a game da sha’anin siyasar kasar inda akasari ke neman karin bayani a kan dokokin jam’iyyu da na zabe na kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: