‘Yansanda a Zambia sun ce akalla mutane 51 sun mutu lokacinda wata motar Bas dauke fasinjoji masu yawa tayi karo da wata babbar motar mai dakon kaya.
Alhamis din nan motocin biyu suka yi karon kan wata babbar hanya kimanin kilomita 100 daga arewacin babban birnin kasar Lusaka.
Kakakin rundunar ‘Yansanda Elizabeth Kanjela, tace yawan wadanda suka halaka a hadarin yana iya karuwa domin masu aikin ceto suna neman gawarwakin da baraguzan motocin biyu suka daddanne su.
Hukumomin kasar suka ce babu bayanai da suka samu nan da nan kan musabbabin wannan hadari.
‘Yansanda suka ce motar fasinjar ta hukumar gidan woyar Zambia, wacce tana dibar fasinja banda aikin raba wasiku.