Majalisar dinkin duniya ta ce sama da mata da ‘yan mata 150 ne, aka yi wa fyade ko kuma aka ci zarafinsu ta hanyar lalata a Sudan ta Kudu.
Ana zargin wasu mutane dauke da makamai, kuma sanye da uniform din sojoji a kusa da Arewacin birnin Bentiu, da aikata aikata wadannan laifukan, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa da Hukumar Asusun Tallafawa kanana yara ta fitar, da kuma hukumar da ke sa ido kan yawan jama’a da kuma ofishin karamin sakataren da ke kula da ayyukan jinkai.
Dukkanninsu sun yi kira ga hukumomi da su fito su yi Allah wadai da wannan aika-aikan.
A makon da ya gabata, kungiyar likitocin kasa da kasa ta "Doctors Without Borders", ta ce mata da ‘yan mata 125 aka yi wa fyade a Bentiu a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani wuri da ake raba abinci.
Kungiyar likitocin ta ce, an kuma kwacewa matan kayayyakinsu na sawa da suka hada da takalma da riguna har da katin karbar abinci.
A cikin wata sanarwa da majalisar dinkin Duniya ta fitar, ta ce an ci zarafin mutane 2,300 a Sudan ta Kudu a farkon shekarer nan ta 2018, mafi aksarinsu kuma mata.
Facebook Forum