Yawan fashi da makami da kashe kashen mutane a birnin Yamai ya sa 'yansanda suka dukufa wurin kawar da wadannan miyagun dabi'u.
Kakakin 'yansandan Yamai Keftain Mainasara Adili Toro shi ya yiwa manema labarai bayani akan yawan mutanen da aka hallaka tun daga farkon wannan shekarar.
Yana mai cewa an samu mutane 11 da aka kashe cikin birnin Yamai. Uku cikinsu a gidajensu aka kashesu yayinda barayi suka kutsa gidansu su yi masu sata.
Bayanai daga 'yansanda sun yi nuni da cewa abubuwan dake faruwa a unguwar Kwaratagi, cikin Yamai, nada da halayyar 'yan daba saboda Adili Toro yace mutane shida da aka kashe a unguwar, uku cikinsu fada ne ya shiga tsaninsu.
Acewar Adili Toro wata uku zuwa yau jami'an tsaro sun cigaba da yin sintiri a unguwar kuma sun samu sun cafke mutane 700. Cikin mutanen 'yansanda sun samu wadanda ake tuhumarsu da laifuka da dama.
Kungiyoyin dake yaki da shan miyagun kwayoyi na alakanta kashe kashen mutane da sace sacen dukiyoyin jama'a da yadda matasa suka tsunduma da shan kwaya.
Malam Ganda Saleh shugaban kungiyar "A Daina" yana mai cewa duk inda aka samu kashe kashe tsakanin samari, a tabbata suna fataucin miyagun kwayoyi ne. Haka kuma idan sun yi sata wajen raba kayan da suka sato, rigima na iya barkewa har ta kai ga suna kashe junansu.
A taron manema labarai 'yansanda sun gabatar da mutane takwas da suka ce ana zarginsu da aikata laifin kisan kai.
To saidai masana sun ce samarwa matasa ayyukan yi ne kadai zai karkata hankulansu daga aikata ayyukan asha.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum