Kotun birnin Yamai ta bude zamanta jiya da shari'ar shugaban kungiyar MPCN Nouhou Arzika, da 'yan fafutikan da aka cafke saboda zarginsu da gudanar da zanga zanga ba kan ka'ida ba.
A karshen makon jiya lauyoyin dake kare 'yan gwagwarmayar suka nuna damuwa akan yadda ake jan kafa wajen soma gabatar dasu gaban alkali domin sanin zahirin laifin da ake zarginsu dashi. Dalili ke nan da lauyoyin ke ganin matakin kotun tamkar wani ci gaba ne kamar yada mai magana da yawun su Martin Sesay Umaru Abdulsalam.
A cewarsa mahukumtar kasar sun ji kiran da suka yi. Can baya lauyoyin sun ce basu amince da alkalin da aka ba shari'ar ba, saboda haka yau sun ga sabon alkali kuma sun amince dashi.
Gabatar da masu fafutikar a gaban shari'a wani mataki ne da ya faranta ran takwarorinsu irinsu Abdulnasir Saidu na NPCR. Kazalika ya ce abu ne ma dake karfafa masu guiwa a ci gaba da kokawar da suka sa gaba. Ya ce su basa tsoron fuskantar shari'a, abunda ba sa so shi ne a yiwa shari'a karan tsaye. Har gobe suna adawa da dokar nan da suke son a kawar saboda zata cutar da jama'a. Abdulnasir yace ya kamata gwamnati ta tausayawa al'ummar kasar ganin irin halin kuncin da suke ciki,amma ba ta kuntata masu da haraji ba.
Bayan an saurare su an mayar da Nouhou Arzika da sauran mutanen da aka cafke ranar 25 na watan Maris zuwa kurkukun Tillabery, yayinda a jiya Litinin, shugaban kungiyar fafutuka da ake kira Wataba Ali Idrisa, dake tsare a gidan kason Filinge, zai bayyana a kotun Yamai. Haka za'a rika jin jami'an dake tsare daya bayan daya har zuwa Juma'a mai zuwa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani
Facebook Forum