A Najeriya, hukumar da ke kula da masu dauke da cutar da ke karya garkuwar jiki wacce aka fi sani da Kanjamau ko Sida, sun bi sahun Majalisar Dinkin Duniya wajen nuna damuwa da yadda bullar cutar coronavirus ta dauki hankalin hukumomi da mahukunta fiye da masu fama da kwayar cutar AIDS.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa, hukumar lafiya ta Duniya wato WHO da Majalisar Dinkin Duniya sun yi hasashen cewa, wadanda suka rasa rayukan su daga kamuwa da cutar HIV ko kanjamau a yankunan Nahiyar Afrika na iya ninka dubu dari biyar idan ba a samar da tsarin kiwon lafiya ga masu kamuwa da cutar ba.
Daya daga cikin masu dauke da cutar wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana wa wakiliyar muryar Amurka halin da suke ciki, inda ya ce, sun fara ganin alamu na raguwar kulawa a fannin jami'an kiwon lafiya da kuma karancin magunguna.
Shi ma shugaban hukumar kula da masu cutar HIV, Dr. Aliyu Gambo ya yi nazarin cewa, dole ne mahukunta su dauki mataki na share wa wadanan mutane hawaye, domin cutar coronavirus tana kokarin ta shiga hakinsu, duk da cewa an fara samun magunguna, amma sai an dore, in ba haka ba magugunan za su iya karanci.
Ita ma jami'ar kiwon lafiya Zainab Abdul ta karyata zargin da ake yi cewa suna gudun marasa lafiya wadanda suka kamu da cutar coronavirus da masu fama da cutar HIV, inda ta bayyana cewa suna sadaukar da rayuwar su domin kula da marasa lafiya a ko ina cikin kasar.
Baya ga irin gudumawar da Majalisar Dinkin Duniya ke ba kasashe masu tasowa a game da irin wadannan cututtuka, yanzu za a sa ido aga irin matakan da kasashen za su dauka domin gani masu dauke da kwayar cutar AIDS ko kanjamau ba su tagayyara ba.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Medina Dauda.
Facebook Forum