Taron wanda shi ne karo na uku da aka gudanar a cibiyar horas da ayyukan ma'adanai da sauran albarkatun kasa ya ta tattaro mutane masana kan ma'adanai daga sassan Najeriya daban daban.
Daraktan cibiyar Umar Saidu Bamali yace manufar taron shi ne su bankado dabarun inganta harkokin ma'adanai yadda kasar zata samu kudaden shiga ta kuma rage dogaro ga man fetur.
Yace zasu kara nunawa jama'a ingancin aikin ma'adanai da kuma nuna masu shi kanshi sana'a ce amma fa sai an tsaya an koyeshi domin ba karatu ne ma kawai ba. Wadanda ma basu yi karatun ba zasu iya nunawa mutum inda ma'adanai suke kuma suna sarafashi amma ba ta hanyar da ta dace ba.
Bamali yace dalili ke nan suke jawo hankalin gwamnati da jama'a da su da suke sana'ar a kara fadakar da mutane bisa abun da suka sani.
Yace shi kanshi ilimi jari ne. Indan mutane sun san yadda zasu sarafa ma'adanan zasu san akwai ma'adanai kala kala da ake abubuwa daban daban dasu.
Injiniya Solomon Dareng kwararre a harakar ma'adanai yace kamata ya yi gwamnati ta samo naurorin da zasu nuna inda ma'adanai suke da sarafasu.domin bunkasa tattalin arziki.Najeriya tana da ma'adanai fiye da dari hudu da hamsin. Kowace karamar hukuma tana da ma'adani kwance a kasa. Idan za'a maida hankali akan ma'adanai kasar na iya mantawa da man fetur. Banda samun kudi da zai shiga aljihun gwamnati matasa zasu samu abun yi maimakon suna yawon shan kwaya.
Shugaban kwamitin ma'adanai a majalisar wakilan Najeriya Samaila Suleiman yace majalisar na kokarin tabbatar da masu hako ma'adanai su bi kai'dodi da sharudda domin anfanin al'umma. Cikin kasafin kudin bana an yi tanadin yadda za'a kawo wadanda suke hakan ma'adanai ba bisa ka'ida ba sun dawo kan tsari.
Ga karin bayani.