Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kenya An Kashe Wani Mai Binciken Sayar da Hakoran Giwa da Karkanda Ta Haramtacciyar Hanya


Wani na shayar da 'ya'yan giwa da madara sanadiyar kashe iyayensu da wasu suka yi a Kenya
Wani na shayar da 'ya'yan giwa da madara sanadiyar kashe iyayensu da wasu suka yi a Kenya

Wasu da ba'a sani ba sun kashe Martin mai binciken masu kashe giwaye da karkandoji saboda sayar da hakoransu a kasuwannin bayan fagge a kasashen Amurka, Congo, Vietnam,Najeriya, Anola, da China da doka ta haramta

An kashe daya daga cikin manyan masu binciken haramtaccen cinikin hauren giwa da na karkanda a fadin duniya.

Jiya Lahadi ne aka sami Esmond Bradley Martin, a mace a gidansa, da alamun an daba masa wuka a wuyansa, a gidansa dake birnin Nairobin Kenya.

An san Esmond, haifaffean Amurka mai shekaru 75 da aiki cikin sirri wanda yake kai ga bankado asirin masu fasakkaurin hauren giwa da kuma masu saya.

Shugabar ma'aikatar kungiyar da take kare muradun dabbobi, Paula Kahumbu tace binciken da Martins yayi ya taimaka wajen tona asirin masu cinikin hauren giwa da karkanda dake Amurka, da Congo, da Vietnam, da Nigeria, da Angola, da China, da kuma Myanmar a baya bayan nan. Aikin shi ne ya tilastawa China, ta hana cinikin Hauren giwa ta haramtacciyar hanya a shekarar 1993.

Binciken da marigayin ya yi shine kuma ya taimaka wajen kawo cinikin hauren giwa ta hanyoyin halal a China, dokar da ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Junairun bana.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG