Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Ajantina mai taka leda a kulob din Barcelona Lionel Messi, ya zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya da karramawar Ballon d'or.
Wannan shine karo na shida da Messi yake lashe kyautar tun daga shekara ta 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, sai kuma wannan shekara ta 2019 inda ya haura kan abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo, na Juventus wanda shi kuma ya lashe sau biyar.
Dan wasan mai shekaru 32 da haihuwa ya taimaka wa kungiyar sa Barcelona, ta lashe kofin Laliga na kasar Spain a shekarar 2018/19, wanda karo na 10 ke nan da kulob din ke daukar kofin tare dashi inda a 2018/19 yaci kwallaye 54, tsakanin kasarsa Ajantina da kuma Barcelona.
Kana a yanzu haka ya buga wasa 700 wa Barcelona inda ya zurara kwallaye 614.
Messi yace wannan nasarar da ya samu karo na shida na zama gwarzon shekara a bangaren kwallon kafa a duniya, ya zama wani sauyi na daban dashi da iyalansa.
Ya na mai farin ciki kan wannan nasarar, ya kuma ce yana fatan zai dauki dogon lokaci yana cigaba da samun nasarori.
Dan wasan Liverpool Vigil Van Dijk, shi ya biyu bayan Messi, sai kuma Cristiano Ronaldo a matsayi na uku.
France Football ce take bayar da Ballon d'Or kowace shekara tun daga 1956, kuma dan wasan kasar Ingila Stanley Matthews ne ya fara lashe kyautar a karon farko.
Facebook Forum