Yajin aikin da ma'aikatan suka shiga yi ya jefa lauyoyi cikin wani halin rudani da kuma wadanda suke jiran hukunci.
Ma'aikatan sun shiga yajin aikin ne saboda fafutikar da suke yi na neman a baiwa fannin shari'a daman cin gashin kai ta hanyar basu kudade kai tsaye kamar yadda wasu jihohi suka yi. Ita ma gwamnatin tarayya ta yi hakan.
Rashin aiwatar da shirin cin gashin kansu ya sa ma'aikatan kotunan suka shafe fiye da watanni shida suna yajin aiki. Lamarin ya haifar da cunkoso a ofisoshin 'yansanda tare da kawo jinkiri wajen yanke shari'a.
Muhammad Usman Karim shugaban kungiyar ma'aikatan kotuna ya bayyana dalilinsu na komawa yajin aiki. Yace gwamnati ta nuna masu halin ko inkula bisa ga yarjejeniyar da suka yi shi ya sa suka koma yajin aikin.
Lauyoyi sun nuna bacin ransu game da wannan dambarwar dake tsakanin ma'aikatan da gwamnatin jihar. Barrister Idris Abdullahi Jalo shugaban kungiyar lauyoyin jihar yace yajin aikin ya jefasu cikin halin tsaka mai wuya. Yace yajin aikin koma baya ne wajen cigaban aiwatar da shari'a.
Ga karin bayani.