Matasan sun ce sun shiga zanga zangar ce domin nuna fushinsu akan yadda aka yi watanni goma sha biyu ba'a biyasu ba duk da koken da suka sha yi.
Matasan dauke da kwalaye sun datse hanyar shiga gidan gwamnati na wani dan lokaci..
Isa Abubakar dake cikin masu zanga zangar yace sun zo ne su karbi kudinsu bisa ga alkawarin da aka yi masu. Yace yanzu shekara daya ke nan babu kudi babu kuma wani bayani. Matasan sun dara dubu daya.
Matasan sun ce sako suka kawo wa gwamna saboda duniya ta ji. Sun kirashi ya ji tsoron Allah ya taimakesu. Suna zargin gwamnatin Neja ta yaudaresu.
Matasan dai na zargin cewa an daukesu aiki kuma suna da wasikar daukan aiki da aka basu. Sun fara aikin ne akan nera dubu goma sha biyar kowane wata. Amma gap da zabe magana ta rikice. Tun daga wannan lokacin a kan yi karin makwanni biyu bisa ga karshen wata kafin a biyasu.
Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ahmed Getso ya fito ya tarbesu. Ya basu zuwa ranar Talata shugabanninsu su zo su sameshi a gidan gwamnati su yi taro saboda lalubo bakin zaren matsala
Ga karin bayani.