Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Kaduna 'Yan Kungiyar Shiya Sun Koka da Kutsen da Suka Ce Jami'an Tsaro Sunyi Masu


Shugaba Buhari da Shugaban Kungiyar Shi'a El Zakzak
Shugaba Buhari da Shugaban Kungiyar Shi'a El Zakzak

Bayan gwamnatin Kaduna ta haramta kungiyar Shiya yau kungiyar ta fito domin yin taron shekara shekra da suka saba yi amma wasu matasa sun fita sun fatattakesu har sun kona wurin taron.

Kungiyar Shiya ta koka da kutsen da tace jami'an tsaro sun yi masu yayin da suka fito taro.

Kungiyar tace an daki 'ya'yanta tare da kona wurin taron.Malam Abdulmummuni Giwa sakataren yada labarai na kungiyar. Yace kowace shekara rana kamar ta yau sukan kaddamar da taron muzahara na ashura wanda yakan faru ne bayan sun gama zaman makoki na kwana goma na tunawa da jikan Annabi Muhammad (SAW)..

Inji Malam Giwa bayan sun gama sai jami'an tsaro suka baibaye wurin da barkonon tsohuwa. Ta bakinsa wasu bata gari suka far masu har aka samu salwantan rayuka. Haka kuma yace makarantarsu bata garin sun lalata makarantarsu.

Saidai rundunar 'yansandan jihar ta musanta salwantar rayuka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG