'Yan matan da aka sace da cigaba da kai hare-hare kullum a wasu kauyuka da kashe mutane da kona garuruwa da sace mutane yasa mutane sun fara bukatar a gudanar da bincike yadda aka kashe makudan kudi akan abun da babu shi yanzu.
Alhaji Saleh Hassan daya daga cikin dattawan arewa da aka tambayeshi ko a binciki rundunar sojan Najeriya sai yace na farko rigimar bata soma da sojan Najeriya ba. Ta soma nae da wasu 'yan tsirarun mutane da aka dauka ba zasu iya yin komi ba. Haka kuma ba'a dauka siyasa zata shigo cikin lamarin ba.
Amma yanzu siyasa ta shigo dumu-dumu. Yace a matsayinsu na dattawan arewa sun je wajen shugaban kasa Jonathan sun fada masa domin basu dauki Boko Haram wata kungiya ce daya ba. Sun dauka akwai Boko Haram iri uku.Akwai ta Yusufiya ita ce ta ainihi wadda yanzu babu ita. Akwai Boko Haram ta gwamnati wacce da ita ake fama. Akwai kuma Boko Haram ta barayi wadanda sun samu zarafi suna shiga su yi sata. Sabili da haka matsalar na nan a gindin gwamnati.
Niyar gwamnati da Boko Haram ba wai domin a zo ana kashe mutane ba ne, amma domin a tsorata mutane da ita idan zabe ya zo su ce sun ci zaben. Wannan kuma talakan Najeriya ya fahimta.
Dangane da makudan kudi da aka kashe domin a wanzar da zaman lafiya a arewa maso gabas Alhaji Hassan yace dole a bincikasu amma binciken zai yi wuya saboda gwamnati ba zata yadda a bincika ba. Domin idan an zo binciken aka ce a binciki soja, shi ma soja zai ce a binciki wani. Idan ba wata sabuwar gwamnati aka samu ba wadda take da tsoron Allah babu abun da zai faru domin Jonathan ba zai bincika ba.
Majalisar kasa ma ba zata bincika lamarin ba domin irin yadda suke tafiya da gwamnati.
Ga karin bayani.