A jihar Bauci dake arewa maso gabashin Najeriya, 'yan bindiga sun kama ma;aikata 'yan kasashe ketare su bakwai, suka kuma kashe maigadi daya a lokacin wani hari da suka kai kan sansanin kamfanin aikin gine gine na wani kora daga lebanon.
'Yan Sanda suka ce 'yan bindigan sun farwa sansanin kamfanin da ake kira Setraco dake garin jama'are cikin jihar Bauci a daren jiya Asabar, daga bisani suka tsere da ma'aikatan da suka kama.
Hukumomi suka ce ma'aikatan da aka kama sun hada da 'yan kasashen Britaniya, da Italiya, da Girka,, da akalla 'yan Lebanon biyu.
Babu wanda ya fito nan da nan ya dauki alhakin kai harin.
Hukumomin Najeriya da farko 'yan bindigan sun kaiwa wani gidan fursina da da ofishin 'yansanda hari a yankin, amma aka fi karfisnu a duka yunkurin biyu da suka yi.