Wani Farfesa ne zai yi tafiya zuwa wata kasa da sai an tsallake kogi kafin a shiga mota. Sai ya tafi gabar teku ya shiga kwalekwale. Sun fara tafiya ke nan sai ya tambayi mai tukin kwalekwale cewa, "mallam ka yi makaranta?" sai mai tukin kwalekwale ya ce, to na dan yi makaranta amma ban yi zurfin karatu ba. Sai Farfesan ya tambaye shi, ka san Biology? sai matukun kwalekwale yace , 'a'a ban sani ba. Sai Farfesan ya sake tambayar shi, ka san Sociology? sai matukin kwalekwale yace , 'a'a ban sani ba. Sai Farfesan ya sake tambayar direban kwakekwalen, ka san Psychology? sai matukun kwalekwale yace , 'a'a ban sani ba. Da jin haka, sai Farfesa ya yi tsaki ya ce wannan akwai jahili, Kai! duniyar nan akwai jahilai. Ashe wannan abu ya yi matukar ba matukin kwalekwale haushi amma ya yi shiru bai ce komi ba, sai da aka kai tsakiyar teku sai ya tambayi Farfesa, " Yallabai ka san kundunbology? sai Farfesa ya ce, 'a,a ban sani ba, sai ya ce to "Tsundumology fa?" sai Farfesa ya ce 'a'a ban sani ba. Sai direban kwale-kwale yace ashe yau zaka mutu a cikin ruwan nan jahili.
Saurari cikakken shirin: