Washington, Dc —
A wannan shirin mun kawo kashi na uku, kuma na karshe na tattaunawar da shirin ya yi da fitaccen dan wasan kwaikwayo da ya shafe sama da shekaru 23 yana wannan sana'ar a Jamhuriyar Nijar.
Mun kuma bada labarin wani Bafullatani da dan Babarbare da fada ya kaure tsakaninsu har ya kai su gaban hukuma.
Saurari cikakken shirin domin jin yadda ta kaya:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.