Yau Talata 9 ga watan Afirilu 2019, za'a dawo cigaba da fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai UEFA Champion League, a matakin wasan daf da na kusa da na karshe (Quarter Final) inda kungiyar kwallon kafa ta Tottenham
za ta karbi bakoncin takwararta Manchester City a sabon filinta da ta gina a kan fam biliyan daya.
Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya ce, wannan gwabzawa da za a yi tsakanin kungiyoyin biyu, na daya daga cikin wasanni mafi muhimmanci a tarihinsa na horar da kwallon kafa.
Wasan zai yi zafi lura da cewa, Manchester City na kan ganiyarta, Inji Pochettino. Inda ake ganin watakila Manchester City ta lashe kofuna hudu a wannan kakar, sai dai kocinta Pep Guardiola ya ce, abune mawuyaci.
Manchester City dai tuni ta lashe kofin Carabao, sannan tana kokarin lashe
kofunan firimiya lig da na gasar kalu bale (FA Cup) na kasar Ingila ga kuma na gasar zakarun Turai.
Tottenham kuwa tana matsayi na hudu ne a gasar Firimiya lig na Ingila da maki 64, a wasannin mako na 32, da ta buga. Har ila yau Liverepool za ta karbi bakoncin FC Porto, a Anfield a matakin wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai.
A kakar wasar da ta gabata Liverpool ta casa FC Porto, da jummular kwallaye 5-0 a zagaye na biyu na gasar ta zakarun Turai.
Za'a buga dukkanin wasannin ne da misalin karfe takwas na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.
Facebook Forum